Game Da Wannan Shafi

Assalamu Alaikum Warahmatullah!

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda cikin ikonsa da yardarsa muke gudanar da dukkan al’amura. Dukkan yabo ya tabbata ga fiyayyen halitta, Shugabammu Annabi Muhammadu Tsira da Amincin Allah Sukara tabbata a gareshi.

Munayi muku barka da zuwa wannan shafi na Kasuwancin Zamani!

Kamar Yadda dunbin jama’a suka sani cewa Kasuwancin Zamani shirine da ake gabatarwa a tashar EXPRESS RADIO 90.3 FM a duk ranar Laraba da misalin karfe 11:00 – 12:00 na rana.

Kasuwancin zamani shirine wanda yake da nufin wayar da kan al’ummah gameda hanyoyin da za’abi akaiga hawa tafarkin aiwatar da harkokin kasuwanci irin na zamani da kuma amfani da sabuwar hanyar nan ta zamani watau YANAR GIZO domin cimma wannan burin. Bisa wadannan dalilai ne mukaga dacewar bude wannan shafi na Kasuwancin Zamani domin ya zamo dandalin baje kolen sana’o’i ko kasuwanci ga ‘yan kasuwannin mu.

Shafin Kasuwancin Zamani ya zo da salon tallata kananan masana’antu, kananan ‘yan kasuwa, masu sana’o’i hannu, Maza da Mata har zuwa matskaita da manyan ‘yan kasuwa a shafin yanar gizo domin bunkasa harkokin kasuwanci kamar yadda cigaban zamani ya kawo.

A takaice shafin Kasuwancin Zamani ya kunshi hanyoyi da dabaru wajen samar da aiyuka ko sana’o’i a shafukan yanar gizo domin magance zaman kashe wando da dumbin matasa keyi, musamman wadanda suka kare karatu babu abin yi.

Har kullum muna godiya a bisa goyon baya da muke samu da ga gareku – wajen bada gudummawa don ganin wannan yunkuri ya cimma nasara.

Kunna wannan na’ura dake kasa domin sauraron tattaunawa tsakanin jami’in wannan shafi da Yusif Ibrahim Yakasai na BBC sashen Hausa 

Update Required To play the media you will need to either update your browser to a recent version or update your Flash plugin.

Godiya Ta Musamman ga Hukumar Gidan Radio Express wadda itace ta dauki nauyin kawo muku wannan shiri na Kasuwancin zamani har tsahon sa’a guda a duk ranar laraba.

Allah Ya Tabbatar mana da Alkhairin dake cikin wannan al’amuri, ya kore mana fituntinun da ke ciki.